logo

HAUSA

Me ya jawo saurin ci gaban cinikin waje na kasar Sin?

2022-08-09 21:25:53 CMG Hausa

Alkaluman cinikin fitar da kayayyaki zuwa ketare na watan Yulin bana, da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar sun sake wuce hasashen da aka yi, inda darajar cinikin ta kai dala biliyan 332.96, adadin ya karu da kaso 18 bisa dari. Sakamakon karuwar cinikin fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje, a watan Yuli, darajar rarar ciniki ta kasar Sin ta kai dala biliyan 101.26, adadin da ya karu da kaso 81.5 bisa dari.

Kafin kasar Sin ta fitar da irin wadannan alkaluma, kamfanin dillancin labaran Reuters ya yi hasashen cewa, karuwar cinikin fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje zai kai kaso 15 bisa dari a watan Yuli, kana, masanin tattalin arzikin da ya yi hira da kamfanin Bloomberg, ya yi hasashen cewa, wannan adadi zai kai kaso 14.1 bisa dari. Amma sakamakon karshe ya shaida cewa, cinikin fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen waje ya ci gaba da habaka cikin sauri a watan Yulin bana.

Wannan al’amari ya shaida cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da bunkasa yadda ya kamata.

Duk da cewa ana fuskantar rashin tabbas a halin yanzu, makomar tattalin arzikin kasar Sin tana da haske, kuma kasar ba za ta sauya aniyar ta ta ci gaba da habaka bude kofa ga kasashen waje ba.

Sergey Lukonin, masani daga cibiyar nazarin tattalin arzikin duniya, da alakokin kasa da kasa a kwalejin ilimin kimiyya ta kasar Rasha ya ce, fadada bude kofarta ga kasashen wajen da kasar Sin take yi, ba amfanar da ita kanta kadai zai yi ba, har ma zai amfani duk duniya baki daya, da samar da karin damammakin cin moriya, tare ga kamfanoni da hajojin kasashen waje. (Murtala Zhang)