An kashe mayakan ’yan aware uku a yankin dake magana da Turancin Ingilishi na kasar Kamaru
2022-08-09 10:20:20 CMG HAUSA
A kalla mayakan ’yan aware uku ne suka gamu da ajalinsu, a lokacin da suka kaddamar da farmaki kan sansanonin soji dake Oku, wani yanki a yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru mai magana da Turancin Ingilishi dake fama da yakin basasa, kamar yadda majiyoyin tsaro na yankin suka tabbatar a jiya.
Wani babban jami'in soji a yankin da ya bukaci a sakaye sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wani kwamandan 'yan awaren ne ya jagoranci harin da aka kai a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ya kira kansa da suna "Babu tausayi".
Jami’in ya ce, mayakan ’yan aware dauke da muggan makamai sun kai hari a sansanonin da ke yankin ta bangarori da dama, a yayin gumurzun da aka shafe yini guda ana ba ta kashi, amma daga baya sojoji suka fatattaki su, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da jefar da gawarwakinsu a wurin taruwar jama’a..
Jami’in ya kara da cewa, shi ma “Babu tausayin" dake zama babban kwamandan 'yan awaren Kamaru, wanda ya yi wa sojoji kwanton bauna, tare da kashe sojoji da dama, ya samu rauni yayin harin, amma ya yi nasarar arcewa. (Ibrahim Yaya)