logo

HAUSA

Sudan na tir da duk wani nau’i na tsattsauran ra’ayi da ta’addanci

2022-08-09 10:02:23 CMG Hausa

 

Shugaban gwamnatin riko ta kasar Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, ya jaddada matsayar kasarsa ta tir da duk wani nau’i na ta’addanci da ra’ayi mai tsauri da aikata laifuffuka.

Abdel Fattah Al-Burhan, ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga wani taron karawa juna sani na kwamitin kula da ayyukan tsaro da bayanan sirri na Afrika (CISSA) da aka yi jiya a birnin Khartoum, mai taken, “Rawar da sauya tunani da gyaran hali ke takawa wajen dakile ayyukan ta’addanci”.

Shugaban na Sudan ya nanata rawar da kwamitin CISSA ke takawa, wajen tinkarar ta’addanci da ra’ayi mai tsauri da laifuffuka tsakanin kasa da kasa da hauren baki tare da shawo kan dukkan kalubalolin tsaro a nahiyar Afrika.

Kwamitin, wanda aka kafa a Nijeriya a shekarar 2004 domin magance kalubalen tsaro a Afrika, yanzu haka, na kunshe da hukumomin tattara bayanan sirri na kasashen nahiyar 54. (Fa’iza Mustapha)