logo

HAUSA

Dangantakar kasar Sin da Taiwan, tamkar ta uba ne da dansa

2022-08-09 19:14:40 CMG Hausa

Wasu mutane na kokarin kwatanta rikicin Ukraine da Rasha da batun yankin Taiwan na kasar Sin. Amma abun da mutane da yawa ba su fahimta ba, batutuwan biyu sun sha bambam da juna.

Ukraine ’yantacciyar kasa ce mai cin gashin kanta a yanzu haka, haka ma kasar Rasha, don haka, rikicin dake tsakaninsu, rikici ne na kasashe makwabta, yayin da Taiwan tun fi azal, ke kasancewa wani yanki na kasar Sin dake karkashin ikonta.

Yayin da rikicin Rasha da Ukraine ke mayar da hankali kan tsarin tsaro a nahiyar Turai, batun Taiwan ya shafi cikin gidan kasar Sin ne. Misali, kamar uba ne da ’ya’yansa, sai wani daga can waje ya ce zai jagoranci yadda ya kamata magidanci ya tarbiyantar ko tafiyar da harkokin ’ya’yansa. A ganina, babu wani uba da ya san ciwon kansa, da zai bari ana tsoma baki cikin harkokin cikin gidansa ko kuma a nemi nuna masa fin karfin kana abun da yake mallakinsa. Tun asali, Taiwan ba kasa ba ce, yanki ne a cikin kasar Sin, don haka, jamhuriyar jama’ar kasar Sin ce ke wakiltar ta a matakin kasa da kasa.

Ban da wannan, atisayen da sojojin ’yantar da al’ummar kasar Sin ke yi a tekun kudancin kasar, ba matakan soji na yaki ba ne, tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro, tare kuma da bayyana karfin kasar Sin na dakile duk wata barazana dake neman ta da rikici a yankunanta ko kawo cikas ga kwanciyar hankalin daukacin kasar. Don haka, duk wani mataki da kasar ta dauka dangane da batun, ta dauke shi ne bisa doron doka, kamar yadda hakkin tsawatarwa ya rataya a kan uba, haka ya kamata kasar Sin ta tsawatarwa Taiwan har ma da masu goya masa baya. (Fa'iza Mustapha)