logo

HAUSA

Cibiyar Luban da ke samar da damammaki ga matasan Habasha

2022-08-08 21:54:12 CRI


Yau da shekaru sama da 2500 da suka wuce, akwai wani babban magini na kasar Sin da aka san shi da suna Luban, wanda ya shahara ne sabo da nau’o’in kayayyakin aiki da ya kirkiro. Ga shi kuma yau bayan shekaru 2500, an samu cibiyoyin koyar da sana’o’i da aka sa musu sunan Luban, wadanda suka samu yabo daga kasa da kasa.

A watan Maris na shekarar 2019, an kaddamar da cibiyar koyar da sana’o’i ta Luban a kasar Djibouti, wadda ta kasance irinta ta farko da aka kafa a nahiyar Afirka, inda aka fara da koyar da aikin kula da layukan dogo, da aikin injiniya na gina layukan dogo da sauransu. Daga baya kuma, bi da bi an kafa cibiyoyin Luban a sauran wasu kasashen Afirka, da suka hada da Kenya, da Afirka ta kudu, da Mali, da Nijeriya, da Masar, da Uganda, da Cote d’Ivoire, da Mardagascar da Habasha, wadanda kawo yanzu suka kai 14.

A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara wata cibiyar Luban da ke kasar Habasha, don samun fahimtar yadda matasan kasar ke koyon sana’o’i a cibiyoyin na Luban.