logo

HAUSA

AU ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai a zirin Gaza

2022-08-08 13:53:25 CMG Hausa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat ya yi Allah wadai da ci gaba da kai hare-hare ta sama da Isra'ila ke yi a yankin zirin Gaza.

A cikin wata sanarwar da kungiyar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, Mahamat ya ce, harin da aka kai kan fararen hula, gami da mamayar da jami'an tsaron kasar Isra'ila suke yi ba bisa ka’ida ba a yankunan Falasdinawa, babban cin zarafi ne ga dokokin kasa da kasa, da kuma kawo cikas ga neman mafita mai dorewa.

Sanarwar ta ce, shugaban hukumar ta AU, ya sake jaddada goyon bayan kungiyar, game da gwagwarmayar kafa halastacciyar kasar Palasdinu mai 'yancin gashin kai da al'ummar Palasdinu suke yi, da kuma gabashin birnin Kudus a matsayin hedkwata. (Ibrahim)