logo

HAUSA

Ziyarar Nancy Pelosi zuwa Taiwan takala ce mai muguwar manufa

2022-08-08 16:58:51 CMG Hausa

A daren Talatar 2 ga watan Agustan shekaran nan ne kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta dira a tsibirin Taiwan na kasar Sin, duk da cewa kasar Sin ta gargadi kasar Amurka tun kafin Nancy Pelosi ta tashi daga Amurka.

Wannan halin dai irin na mai kunnen kashi da Amurka ta dauka na shirya ziyarar kakakin majalisa Pelosi dai abu ne wanda ya keta 'yancin mulkin kasar Sin da tsokana da shiga sharo ba shanu a harkokin cikin gidan kasar.

Tun farko dai shuwagabanin kasashen biyu na Sin da Amurka wato Xi Jinping da Joe Biden sun tattauna a wayar tarho, inda shugaba Xi ya ja kunnen kasar ta Amurka da cewa duk wanda ya yi wasa da wuta to ya tabbatar da shi za ta kona.

Sanin kowa ne dai cewa kasar Sin daya ce tak a duniya kuma Taiwan yanki ne na kasar, a kan wannan, kasar Amurka ma ba ta musanta haka ba domin Sin da Amurka sun cimma yarjejeniyar kulla huldar diplomasiyya a shekarar 1978, inda Amurkar ta amince da gwamnatin jamhuriyar jama’ar Sin a matsayin halastacciyar gwamnati daya kacal na kasar ta Sin, kuma jama’ar Amurka za ta kiyaye hulda da jama’ar yankin Taiwan ta fannonin al’adu da ta kasuwanci da sauransu, amma ban da ta sassan gwamnati.

Taiwan dai tsibiri ne kuma yanki ne a karkashin jamhuriyar jama'ar Sin wanda yake kudu maso gabashin kasar. Mutanen Taiwan dai Sinawa ne kuma yarensu da al'adunsu duka na Sinawa ne.

Haka kuma kamar yadda muka sani, Taiwan ba kasa mai zaman kanta ba ce kuma ba ta da mazauni a majalisar dinkin duniya MDD ko a kungiyoyin kasa da kasa irin na gwamnati, don haka ma ne, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya nuna rashin jin dadinsa da ziyarar Pelosi wadda take neman ta da zaune tsaye da kawo rudani a zaman lafiya a yankin gabashin Asiya da ma duniya baki daya. Babban sakatare Guterres ya yi bayani cewa za a tsaya tsayin daka kan kudurin kasancewar kasar Sin daya ce tak a duniya.

Kasashe dai fiye da 160 ma suka yi tir da ziyarar Pelosi da nuna goyon bayansu ga kasar Sin da kuma bayyana cewa ziyarar ta keta dokokin kasa da kasa da manufar nan ta kasar Sin daya ce tak a duniya kuma Taiwan yanki ne na kasar Sin.

Wannan ziyara dai a ganina na mai lura da harkokin kasashen waje, babban kuskure ne kasar Amurka ta tafka, kuma takala ce da yin katsalandan a harkokin cikin gida na kasar Sin. Haka zalika, abin lura ne Amurka na yin amfani da gurbatacciyar siyasa a yankin Asiya domin wata manufarta. A sakamakon sa ido da katutu da Amurka ke yi a yankin ya sa kasashe da dama suna yin tir da halayenta na neman fitina.

Hakazalika ban da ta da zaune tsaye da tsokana da wata manufa ban ga amfanin da ziyarar Pelosi za ta kawo wa yankin Taiwan ba da kawo halin zaman doya da man ja a huldar da ke tsakanin kasar Sin da Amurka. A yanzu haka dai wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin kasar Sin da Amurka a yayin da kasar Sin ta yi martani ta hanyar dakatar da wasu yarjejeniyoyi da ake yi tsakanin kasashen biyu a baya. Ita ma Nancy Pelosi ta samu nata a yayin da kasar Sin ta kakaba mata tare da iyalanta takunkumai da suka dace da tanadin dokokin jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Wannan dai duk abubuwa ne wadanda ya kamata kasar Amurka ta san cewa kasar Sin ba za ta zauna ta yi shiru ba idan aka ci zarafinta ba.

Ya kamata kuma Amurka ta lura cewa Allah wadai da kasashe suka yi a kan wannan ziyara wani abu ne da zai rage mata girmamawa a idon duniya baki daya saboda abin da zai haifar sakamakon ziyarar zai iya shafar kasashen duniya da ba su san hawa ba bare sauka ba. (Lawal Sale)