Tobi Amusan: Jajircewa da aiki tukuru ta sanya kwalliya biyan kudin sabulu
2022-08-08 09:06:46 CMG Hausa
Daga unguwar Ijebu Ode dake wajen garin birnin Ikko, matashiya Tobi Amusan, ta kai ga kololuwar matsayi na duniya a fannin gasar tseren mata, inda bayan haye wahalhalu da dama, ta kai ga kasancewa gwarzuwar ‘yan wasan tsere da tsallake shinge ta duniya. Bibiyar nasarar da Tobi Amusan daga tarayyar Najeriya ta samu, abu ne mai ban sha’awa.
Baya ga kasancewa wannan ne karon farko da Najeriya ta taba cimma nasarar lashe lambar zinari, a wannan gasa ta tseren mata ta duniya baki daya; haka kuma wannan ne karon farko da aka buga taken kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, daga dandalin gabatar da bayanai game da wannan muhimmiyar gasa ta kasa da kasa.
Yayin da ake buga taken Najeriya, hawaye sun kwararowa Amusan. A wurin ta, lokaci ne na matukar farin ciki, wanda ya tabbatar da gajiyar da aiki tukuru na shekaru da dama da ta gudanar ya haifar mata, wato dai kwazon ta bai tafi a banza ba. Kamar yadda wani bangare na taken Najeriyar ke cewa “Aiki tukuru na ‘yan mazan jiyan mu, ba zai taba zama a banza ba”. Yayin da ake buga wannan take, Amusan ta tuno yadda ta fuskanci, radadi, da rashin nasara, da koma-baya, da bacin-rai na tsawon shekaru.
A cewar Tobi, wadda ta fashe da kuka bayan nasarar ta, ta ce ta yi bakin ciki matuka, kasancewar ba ta samu damar wakiltar Najeriya a gasar Olympics ta birnin Tokyo ta shekarar 2020 ba. Ta ce ta rasa damar wakiltar kasar ta a gasar da ta wuce, tare da shiga tsere da tauraruwar ta a wasan tsere wato Glory Alozie, wadda suka hadu da juna kwana guda kafin Amusan ta lashe gasar ta bana.
Kafin hakan, Amusan ta taba lashe tseren mita 100, a gasar share fagen gasar Olympics da aka gudanar a kwalejin fasaha ta Yaba dake jihar Lagos. Bayan gasar ta ma gano cewa, na’urar da aka yi amfani da ita wajen fadar sakamakon wa’adin tseren ta ba ta yi aiki yadda ya kamata ba.
Ta lura cewa, na’urar agogon hannun ta ta nuna cewa, ta kammala gudun ta ne cikin dakika 12.30, wanda ya kai matsayin wa’adin da Gloria Alozie ta taba kaiwa a gasar nahiyar Afirka, inda a shekarar 1998 Gloria din ta kammala tseren na mita 100 cikin dakika 12.44.
Yayin wata ganawa da ‘yar jarida Teja Onojaife, Tobi ta ce mai horas da ita wasan tsere, kuma ‘yar wasan da ta taba shiga gasar Olympics har karo 3 daga kasar Jamaica, ta kuma lashe gasar tseren mita 100 a gasar kasashe renon Ingila ta shekarar 2002 Lacena Golding-Clarke, ta bani kwarin gwiwa. Tobi ta ce, Lacena Golding-Clarke ta fada min cewa, “Ki yi aiki tukuru. Ki nunawa duniya za ki iya, idan ba su bayyana nasarar ki a gida ba, za a bayyana a waje”.
Kwarin gwiwar da ta samu daga kocin ta, ya sanya ta kawar da zuciyar ta daga rashin nasarar da ta fuskanta, na rashin ba ta lambar yabo ta Afirka, inda ta shiga babbar gasa ta duniya, ta kuma kafa tarihin doke wadanda suka taba samun nasara a irin wannan gasa daga nahiyar Afirka.
Yanzu dai Tobi ta karya matsayin bajimta bayan shan kaye a baya. Da farko dai ta karya matsayin bajimtar Alozie AR, a zangon karshe na tseren “Wanda Diamond League” wanda aka yi a bara a birnin Zurich, inda a baran ta kammala tseren ta cikin dakika 12.42, ta kuma kara samun wata nasarar cikin tsaren da ta gaba a dakika 12.40, yayin bude gasar kasa da kasa ta Oregon, na Amurka.
A wannan karon ma ta kafa tarihin zama ‘yar Afirka ta farko, kuma ‘yan Najeriya mafi gudu a tarihin gasar. Yanzu haka kuma, Amusan ta maida hankali ga cimma karin nasarori, bayan kafa tarihin zama ‘yan Najeriya ta farko da ta lashe lambar zinari a gasar tseren kasa da kasa.
Tobi Amusan, ta zamo ‘yar Najeriya ta farko da ta taba lashe zinari a gasar tsere ta duniya, inda ta kammala tseren ta na bana cikin dakika 12.6. Kuma karo na biyu da Amusan ta karya matsayin bajimta a dare daya, inda ta samu karin nasara sama da dakika 12.12, da ta yi a zangon wasan kusa da kusan na karshe; wanda kafin Amusan, ‘yar tseren kasar Amurka Kendra Harrison ta kafa na ta tarihin cikin dakika 12.20.
Duk da wannan nasara da ta samu a matsayin ‘yar Afirka, yayin gasar kasashe renon Ingila, da kuma fatan kafa karin tarihi a nan gaba, Tobi ta sha fuskantar manyan koma baya a gasannin Olympics, da na kasa da kasa, wadanda ta taba halarta a baya.
A baya ta fara shiga gasanni cike da nishadi, inda a gasar matasa ta cin kofin Afirka ta shekarar 2013, wadda ta gudana a birnin Warri na kudancin Najeriya, ta lashe lambar azurfa. Ta kuma taba lashe lambar Zinari a gudun mita 100, yayin karamar gasar ‘yan wasan motsa jiki ta 2015, wadda ta gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
A shekarar 2015 kuma, yayin da take da shekaru 18 da haihuwa, ta lashe tseren mita 100 da lambar zinari. Kaza lika ta lashe wata gasa ta kwalejojin kasa da kasa.
A shekarar 2016, yayin da ta fara karatu a jami’ar Texas UTEP, ta halarci gasar C-USA, inda ta zo na 2 cikin daukacin daliban jami’ar mata da aka baiwa lambar gasar C-USA ta ‘yan wasan tseren mata mafiya kwazo a tarihin jami’ar, tun bayan da jami’ar ta fara shiga gasar ta C-USA. Har ila yau, ta yi nasarar lashe gasar NCAA ta shekarar2017, inda ta kammala tsere cikin dakika 12.57.
Tobi ta fara yin fice a wajen nahiyar Afirka ne a shekarar 2018, lokacin da ta shiga gasar kasashe renon Ingila da aka yi a Australia. A wannan karo ta zarge zakarar gasar ta shekarar 2015 wato Danielle Williams, inda ta lashe lambar zinari. Kana ta lashe lambar azurfa a gasar gudun mita 100 ta ‘yan wasa 4 tare da abokan wasan ta Joy Udo-Gabriel, da Blessing Okagbare, da Rosemary Chukwuma.
Daga baya cikin dai shekarar ta 2018, Tobi ta lashe gasar Afirka ta farko, wadda aka yi a birnin Asaba na kudancin Najeriya. Ta karbi lambar zinari ta ‘yan wasa 4 a dai wannan gasa ta gudun mita 100.
A matsayin ta na ‘yar wasa da ta fara shiga gasanni cikin himma da karsashi, da farko ta sha kaiwa kusa da nasara, amma sai ta gamu da cikas. Bayan cimma nasarar lashe gasar kasa da kasa ta shekarar 2022, Tobi ta ce “Na sha zuwa kusa da nasara, na samu matsayi na hudu, na hudu, na hudu, haka dai. Har daga karshe dai na kai ga nasara”.
A gasar tseren duniya ta 2019 wadda ta gudana a birnin Doha na kasar Qatar, matashiyar ta kai ga kammala tseren mita 100 cikin dakika 12.48 a zangon farko na gasar. Washe gari kuma yayin wasan kusa da kusan na karshe, ta sake kai wannan matsayi kafin daga bisani ta cimma matsayi na 4, a zagayen karshe cikin dakika 12.49. Kaza lika yayin gasar kasa da kasa ta 2017 ta kammala a matsayi na 14, yayin da a shekarar 2019 ta kammala a matsayi na 4.
Yayin gasar Olympic ta birnin Tokyo da aka yi a bara, ta yi na 4 da dakika 12.60. bugu da kari, a gasar Rio ta kasar Brazil, Tobi ta kammala tsere a matsayi na 14, bayan kaiwa ga matsayin wasan kusa da kusan na karshe.
A ranar 9 ga watan Satumban shekarar 2021, yayin wasan karshen “Wanda Diamond League” na birnin Zurich, Tobi ta yi nasarar kammala tseren mita 100 cikin dakika 12.42, lamarin da ya kai ta ga lashe kofin “Diamond League”, bayan rashin nasarar ta a gasar Olympics ta Tokyo. Bisa nasarar lashe kofin “Diamond League” Tobi ta zamo ‘yar Najeriya ta farko da ta daga wannan kofi. Ta kuma karya matsayin bajimtar da Glory Alozie ta kafa, na kammala tsere a dakika 12.42, sama da tarihin da Glory ta kafa na dakika 12.42.
Amusan ta bude gasannin ta na 2022 da lashe gasar “Diamond League” ta birnin Paris, inda ta kafa tarihi na Afirka, bayan gama tsere cikin dakika 12.41, sama da dakika 0.01 da aka taba samu a baya.
Yayin gasar tseren mita 100 da tsallake shinge na bana da ya gudana a Mauritius, ta kare kambun ta, inda ta kammala tsere cikin dakika 12.57 (ko da yake iska mai karfi ta taimaka mata yayin tseren). Har ila yau, ta shiga gasar tseren mata 4 na mita 100, ta kuma lashe zinari. Kaza lika ta lashe zinari a gudun mita 100 da tsallake shinge a gasar kasar Finland.
Amusan ta zarce ‘yar tseren Jamaica Britany Anderson, inda ta kammala tseren ta cikin dakika 12.57, sama da Anderson wanda ta kammala cikin dakika 12.59. Nasarar gasar Finland ta share mata fagen cimma nasarar da ta samu a gasar Oregon.
Daga kusan samun nasara, zuwa cikakkiyar nasara, Amusan mai shekaru 25, ta gama tseren ta a dakika 12.12, inda ta rage kusan dakika 0.1, sama da tarihin da ta taba kafawa a wasan kusa da na kusan karshe na gasar Oregon, kafin kuma ta kai ga lashe zinari a gasar tseren mata ta kasa da kasa da ta gudana a Amurka a baya bayan nan.