logo

HAUSA

Yin Jianmin: Kokarin taimaka wa matan da ke karkarar kasar Sin wajen yakar talauci

2022-08-08 08:53:58 CMG Hausa

Yin Jianmin, shugaba kuma mai kamfanin fasahohin ayyukan gona na zamani wato Xinyuan Modern Agricultural Technology Development Company, dake birnin Lanzhou, ta shafe shekaru 20 da suka gabata, tana taimakawa masu bukata, musammam mata, a yankunan karkarar lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar Sin, wajen yakar talauci da cimma burikansu ta hanyar sana’o’i na musammam da kirkiro guraben ayyukan yi.

Akwai yara 4 a gidansu Yin Jianmin mai shekaru 62, dake birnin Dandong na Lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin. Mahaifinta, wanda dan JKS ne, da ya samu lambar yabo ta ma’aikaci abun koyi na kasa, ya kan koyawa Yin da ‘yan uwanta wasu kyawawan dabi’u.

Yin ta kan tuna cewa, iyayenta ba su taba korafi game da yanayin rayuwarsu ba, kuma su kan taimakawa sauran mutane, ko da kuwa mutanen sun fi su wadata.

A kusan karshen shekarar 1980, Yin ta ajiye aikinta na samar da lantarki a Dandong, domin neman yadda za ta samu arziki a lardin Guangdong na kudancin kasar Sin. kuma bayan shafe shekaru tana aiki tukuru, ta samu kudin da take bukata.

A shekarar 2000, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufar raya yankin yammacin kasar. Saboda yakinin da take da shi da neman sanin yadda yankin zai kasance, Yin ta kaura zuwa yankin a wannan shekarar. Ta kuma kuduri niyyar taimakwa mutanen karkara.

Yayin da take kammala rangadi a wasu yankuna masu fama da talauci a lardunan Gansu da Qinghai, sai ta kamu da son wannan yanki, wadanda har a lokacin, mutane ke rayuwa cikin talauci duk da dimbin albarkatun da yankin ya mallaka. Yin ta yanke shawarar sauya rayuwar mutanen ne yayin da ta tsaya a bakin Rawayen Kogi.

A shekarar 2001, ta kafa kamfanin samar da gas na Xinyuan Natural Gas Co. Ltd, a Honggu, wata gunduma dake Lanzhou, babban birnin lardin Gansu. Yin da ma’aikatanta kan je gida-gida, domin neman kwastamomi da tattauna alfanun amfani da gas.

A karshe dai sun samu kwastoma na farko, wanda duk da yana sha’awa, ya yi shakku game da karfin kamfanin na shimfida bututun iskar gas daga Qinghai zuwa Gansu.

Ga mamakin abokan huldarsa, a karshe, kamfanin ya shimfida bututun. Kuma a yau, kamfanin na da ma’aikata sama da 300, kana ya mallaki kadarorin da darajarsu ta kai sama da yuan biliyan 1, kwatankwacin dala miliyan 154.

Yayin shimfida bututu, Yin ta ziyarci sama da kauyuka 200 dake kan hanyar da bututun ya ratsa.

A nan ta fahimci cewa, sai ta hanyar gabatar da sana’o’i da shirye-shiryen yaki da talauci ne mutane za su iya fitar da kansu daga kangin fatara, su more rayuwar jin dadi tare da tsayawa da kafafunsu.  

Don haka, Yin ta kaddamar da wata harkar kasuwanci a Honggu, harkokin sun hada da kiwon raguna da noman kayayyakin marmari da na lambu, a wani yanayi na kare muhalli.

Yin ta yi nasarar samar da damarmakin ayyukan yi sama da 1,000 ga mutanen kauyukan, kuma nasarar da kasuwancin ya samu ta karfafa yakinin Yin na rage talauci ta hanyar kirkiro sana’o’i .

A shekarar 2014, Yin ta kafa kamfanin fasahohin ayyukan gona na Xinyuan, domin taimakawa shirin yaki da talauci na gwamnatin kasar Sin a fadin kasar.

A baya, gundumar Dongxiang mai cin gashin kansa dake lardin Gansu, ta kasance yankin a matakin kasa da fatara ya yi wa katutu. A shekarar 2018, Yin ta zuba jari a wasu gonakin kiwon raguna 2 a Dongxiang, kuma ta karfafawa mutanen yankin samar da wani tambari na naman rago mai inganci.

Zuwa watan Yunin 2021, Yin ta ware yuan miliyan 8.56, kwatankwacin dala miliyan 1.32, a matsayin ribar kasuwancinta na kiwon raguna, ga iyalai matalauta. Wannan kudin ya taimakawa iyalai 11,000 tserewa talauci.

Saboda dimbin kokarinta, tambarin naman rago na Dongxiang ya samu karbuwa a fadin kasar, har ma ana bayar da rahoto kansa a gidan talabijin na kasar wato CCTV.

Yayin ziyararta ta farko a wani kauye dake gundumar Dongxiang, Yin ta gano cewa, galibin matan kauyen na kunyar zantawa da mutanen da ba su sani ba. Yin ta yi ittifakin cewa, sai ita da sauran mutane sun samar da damarmakin aikin yi ga matan ne kadai, za a iya fitar da kauyen daga kangin talauci.

A don haka, a shekarar 2018, Yin ta samar da yuan miliyan 38, kwatankwacin dala miliyan 5.85, wanda ta yi amfani da shi wajen kafa wani kamfanin samar da laimar kwado a DongXiang. Kamfanin ya yi hayar matan wurin domin su noma laimar kwado. Inda suke aikin karba-karba.

Har ila yau, Yin ta kuma karfafa musu gwiwar ci gaba da neman ilimi, da kuma neman kwarewa a fannin fasahohin gona.

Yin ta samar da kyawawan sauye-sauye da dama ga rayuwar matan kauyen, wadanda su ma suka dauke ta tamkar ‘yar uwarsu.

Da taimakon kungiyar mata ta kasar Sin, wadda ta kulla hadin gwiwa na musammam da Zhangxian, wata gunduma dake Gansu, a wani shirin yaki da talauci, a shekarar 2021, Yin ta bude cibiyar sarrafa laimar kwado a gundumar, duk da karancin kayayyakin gini da na aiki da annobar COVID-19 ta haifar, wannan kamfani ya samar da guraben ayyuka 1,000 ga matan gundumar.

Baya ga kokarin raya tattalin arzikin yankuna masu fama da talauci a Gansu, Yin ta taimaka wajen shiryawa da tafiyar da shirye-shiryen samar da tallafi a shekarun baya-bayan nan.

Makarantar Ganping na da zaune ne a cikin tsaunikan gundumar Lintao. A 2012, Yin ta bayar da gudummuwar kujeru da tebura ga makarantar, kana ta samar da yuan 300,000, kwatankwacin fiye da dala 46 domin sake gina wasu ajujuwa.

Tun daga sannan, Yin ta kan ziyarci makarantar a kowanne zangon karatu, kuma ta kan kai wa dalibai takardu da sauran kayayyakin karatu. Ta kuma gayyaci daliban zuwa birnin Beijing domin su kara bude idanunsu.

Zuwa yanzu, Yin ta taimakawa sama da dalibai 600. Kuma yanzu haka, galibinsu sun shiga harkokin taimakawa mutane mabukata.

Yin ta dauki ma’aikatanta tamkar ‘yan uwa, kuma ta kan taimaka musu kara sakewa da kasancewa cikin annashuwa yayin da suke wajen aiki.

Misali, Yin ta kan aike da kyaututtuka ga yaran ma’aikatanta gabanin ranar yara ta duniya, kuma ta kan ci abinci tare da ma’aikatan da ba su yi aure ba a lokacin bikin bazara, wato bikin sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa.

A shekarar 2016, gidauniyar tallafi ta Lanzhou ta kafa wani asusu na musammam da sunan Yin, domin taimakawa wajen samar da kudin makarantar dalibai da na kiwon lafiya da sauran bukatun masu fama da talauci. Cikin shekaru da dama da suka gabata, Yin ta bayar da gudunmuwar kusan yuan miliyan 24, kwatankwacin dala miliyan 3.69 ga asusun.

Yin na alakanta nasarorin da ta samu daga goyon bayan da gwamnatin kasar da ma al’umma suka ba ta. ta ce, “rayuwar dan kasuwa za ta kara ma’ana ne idan ya hada burikansa da sadaukarwa wajen taimakawa sauran mutane da kokarin raya harkokin al’umma”.(Kande Gao)