logo

HAUSA

MDD da Masar sun shiga tsakani domin tsagaita bude wuta tsakanin Palestinu da Isra’ila

2022-08-06 16:28:52 CMG Hausa

A cikin ‘yan kwanakin baya bayan nan, rikici ya kara tsanani tsakanin Palestinu da Isra’ila, don haka MDD da kasar Masar sun shiga tsakani cikin gaggawa a jiya Juma’a, domin kawo karshen yanayin tashin hankali a zirin Gaza.

Manzon musamman kan batun Gabas ta Tsakiya na MDD Tor Wennesland, ya fitar da wata sanarwa jiya, inda ya bayyana cewa, yanzu MDD tana tuntubar bangarorin dake gwabzawa da juna, domin hana tsanantar rikicin, wanda zai jefa fararen hula dake rayuwa a zirin Gaza cikin halin ni ‘yasu.

Hakazalika, rahotannin kafofin watsa labarai na Masar sun ruwaito cewa, wani jami’in kasar ya taba bayyana cewa, Masar tana tuntubar Palestinu da Isra’ila, domin shawo kan yanayin zaman dar dar da zirin Gaza ke ciki.

Rahotanni na cewa, jiragen saman yaki na Isra’ila sun kai wa zirin Gaza hari ta sama a jiya, kuma har boma bomai sun fashe a wasu sansanonin kungiyar masu Jihadi dake zirin Gaza, inda Palestinawa 10 suka rasa rayuka, wasu mutane sama da goma kuma suka ji rauni. Daga baya kuma, dakarun kungiyar masu Jihadi, sun harba makaman rokoki ga yankunan tsakiya da kudancin Isra’ila domin mayar da martani. (Jamila)