logo

HAUSA

Kasar Sin ta musanta zarge-zargen Amurka game da atisayen da take yi a kewayen Taiwan

2022-08-06 19:07:49 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a Amurka, Qin Gang, ya musanta zarge-zargen Amurka, game da matakan martani na atisayen soji da Sin ta dauka dangane da ziyarar da shugabar majalisar wakilan Amurkar, Nancy Pelosi ta kai Taiwan.

Qin Gang ya musanta zarge-zargen ne bayan sammacin da majalisar tsaron kasa ta fadar White House ta aike masa.

Kasar Sin ta sanar da aiwatar da jerin matakai, ciki har da atisayen soji da harba makamai a kewayen Taiwan, daga ranar 4 zuwa 7 ga wata.

Sanarwar da ofishin jakadancin Sin a Amurka ta fitar, ta ce duk da gargadin da Sin ta nanata yi kafin lokacin, sai da Amurka ta sa Nancy Pelosi ta ziyarci Taiwan. Tana mai cewa, wannan barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin kewayen zirin Taiwan da kuma dangantakar Sin da Amurka, don haka, dole Washington ta dauki alhakin yanayin da ake ciki yanzu.

Sanarwar ta kara da cewa, zargin da Amurka ke yi cewa Sin ta tsananta zaman dardar a yankin, ba shi da tushe kuma karya ce. Shaidu sun tabbatar da cewa, Amurka ce ke yin karan tsaye ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan da ma yankin baki dayansa. (Fa’iza Mustapha)