Amurka ce ke yi wa zaman lafiya a zirin Taiwan barazana
2022-08-06 18:58:48 CMG Hausa
Yayin ziyararta a yankin Taiwan na kasar Sin, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta yi ikirarin cewa, ziyarar na da nufin inganta zaman lafiya a yankin, wanda ya yi daidai da abun da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 suka bayyana cikin sanarwarsu, inda kuma suka soki matakan martani da tsaron kai da Sin ta dauka, suna cewa matakan za su haifar da zaman dardar a yankin, tare da ikirarin a warware sabani cikin lumana.
Yanzu, masu haddasa fitina sun zama masu kare zaman lafiya, kuma sun jikirta gaskiya da karya domin nuna yatsa ga masu halaltattun ‘yanci. Sun hada kai suna kokarin yaudara da karkatar da hankalin duniya ta hanyar juya batun. Amma kuma sun yi wa yanayin bahaguwar fahimta, kana sun raina karfin ra’ayin jama’a.
Cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, daruruwan kasashe a fadin duniya ne suka bayyana ra’ayoyi da matsayarsu ta nacewa ga manufar Sin daya tak a duniya, tare da goyon bayan kasar wajen kare cikakken ‘yanci da ikon mallakar yankunanta. Kasashen duniya na goyon bayan kasar Sin ne saboda sun ga yadda ake kokarin ta’azzara yanayin zirin Taiwan. Ziyarar da Pelosi ta kai yankin, shiryayye ne dake da nufin tsokanar kasar Sin, kuma takala ce ta siyasa domin amfani da Taiwan din wajen juya kasar Sin. Tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, ya saba da dokokin kasa da kasa da kuma ka’idar huldar kasa da kasa. Bugu da kari, Amurka ce ke da alhakin ta’azzarar yanayin zirin Taiwan. (Fa’iza Mustapha)