logo

HAUSA

NDLEA ta kona sama da kilogram dubu 560 na haramtattun kwayoyi da ta kama

2022-08-05 11:13:41 CMG Hausa

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), ta yi nasarar kona sama da kilogram dubu 560 na miyagun kwayoyi a jihar Legas, cibiyar tattalin arzikin kasar, adadi mafi yawa da aka lalata a cikin shekaru 32 na tarihin kafuwar hukumar.

Da yake jawabi a yayin wani biki da aka gudanar a yankin Badagry da ke jihar Lagos, shugaban hukumar ta NDLEA, Mohamed Buba Marwa ya ce, magungunan da aka lalata, na daga cikin nau'in haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogiram miliyan 3.5 da aka kama a fadin kasar tun daga watan Janairun shekarar 2021, ciki har da hodar iblis, da heroin, da methamphetamine, da tabar wiwi da sauransu.

A cewar Marwa, daga watan Janairun shekarar 2021 zuwa yanzu, hukumar ta NDLEA ta kama sama da mutane 17,647 da suka aikata laifukan ta’ammali da miyagun kwayoyi, inda kotu ta yankewa 2,385 daga cikinsu hukunci. (Ibrahim Yaya)