logo

HAUSA

Sudan ta Kudu ta kara wa'adin gwamnatin rikon kwarya da shekaru 2

2022-08-05 11:11:53 CMG Hausa

 

Jiya ne, bangarorin gwamnatin Sudan ta Kudu suka tsawaita wa'adin gwamnatin rikon kwarya da karin shekaru biyu.

Shugaba Salva Kiir ya ce, gwamnatinsa ba ta son tsawaita wa'adin gwamnatin rikon kwaryar don ci gaba da zama a kan karagar mulki ba, illa dai shirya kasar domin gudanar da zabe da zai kai ga mika mulki cikin lumana. (Ibrahim Yaya)