logo

HAUSA

Ministocin wajen ASEAN: RCEP ta ba da gudummawa ga dabarun farfado da yankin

2022-08-05 15:01:12 CMG Hausa

Ministocin harkokin wajen kasashen ASEAN sun bayyana cewa, yarjejeniyar cinikayyar yanki cikin ’yanci da ake kira RCEP a takaice, za ta bayar da muhimmin taimako ga dabarun farfado da kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya.

Ministocin wadanda suka bayyana hakan cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan taronsu karo na 55 (AMM) da aka gudanar a Phnom Penh, babban birnin Cambodia, sun yi maraba da yadda yarjejeniyar ta fara aiki tun daga ranar 1 ga Janairu, 2022.

Yarjejniyar ta RCEP dai ta kunshi kasashe 15 dake yankin Asiya da Pacific, ciki har da kasashe membobin ASEAN 10, da suka hada da kasashen Brunei, da Cambodia, da Indonesia, da Laos, da Malaysia. Sauran sun hada da Myanmar, da Philippines, da Singapore, da Thailand da Vietnam, da abokan cinikinsu guda biyar, wato kasashen Sin, da Japan, da Koriya ta Kudu, da Australia da kuma New Zealand.

Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin manyan yankunan, za ta kawar da kusan kashi 90 na haraji kan kayayyakin da ake yi ciniki a tsakanin kasasahen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar cikin shekaru 20 masu zuwa. (Ibrahim Yaya)