logo

HAUSA

Tsokacin da Amurka ke yi game da yanayin Taiwan na nuna girman kanta da danniya da rashin sanin ya kamata

2022-08-04 19:58:28 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce tsokacin da jami’an Amurka ke yi game da yanayin Taiwan, na jikirta karya da gaskiya, wanda kuma ke nuna yadda take ci gaba da nuna girman kai da danniya.

Hua ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau, a lokacin da take amsa tambayar da wani dan jarida ya yi mata game da furucin wani jami’in Amurka dake cewa, hakkin yanayin da ake ciki a zirin Taiwan da tankiyar dake tsakanin Sin da Amurkar, ya rataya ne a wuyan kasar Sin.

Hua Chunying ta kuma jaddada cewa, Amurka ce kadai ke da alhakin yanayin zaman dardar da ake ciki a zirin Taiwan. Haka kuma, musababbin shi ne, Nancy Pelosi ta nace wajen ziyartar yankin ne saboda wasu muradu na son kai da suka yi mummunar keta manufar kasar Sin daya tak. (Fa’iza Mustapha)