logo

HAUSA

Gwamnatoci da dukkan bangarorin al’ummar Afrika na goyon bayan Sin kan batun Taiwan

2022-08-04 20:48:04 CMG Hausa

Bayan ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi ta kai Taiwan, gwamnatoci kasashen Afrika da dukkan bangarorin al’ummar Afrika, sun bayyana goyon bayansu tare da amincewa da matsayar kasar Sin da ma batutuwan dake ci mata tuwo a kwarya.

Da yake ganawa da jakadan Sin a Congo(Brazzaville), Ma Fulin, ministan harkokin wajen Congo, Jean Claude Gakosso, ya ce Taiwan wani bangare ne na Sin, kuma batu ne na cikin gida, haka kuma ya kamata kowacce kasa ta girmama hakan. Yana mai cewa, Congo na goyon bayan matakan kasar Sin na kare ‘yanci da yankunanta.

A nata bangare, kakakin ministan labaran Zimbabwe, Monica Mutswagwa, ta ce ziyarar Pelosi a Taiwan, laifi ne kuma takala ce da ta keta manufar kasancewar Sin daya tak a duniya.

Ofishin jakadancin Eritrea a Sin kuwa, sanarwa ya fitar, inda ya bayyana adawa da ziyarar ta Pelosi, tare da bayyana goyon bayan kasar ga matsayar kasar Sin kan Taiwan. (Fa’iza Mustapha)