logo

HAUSA

Mnangagwa: Zimbabwe za ta ci gaba duk da takunkuman da kasashen yamma suka kakaba mata

2022-08-04 10:21:43 CMG Hausa

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya sha alwashin ci gaba da kokarin ganin kasarsa ta bunkasa. Yana mai gargadin cewa, kasashen yammacin duniya da suka kakabawa kasarsa takunkumai ba za su yi nasara ba, a makircinsu na kawo cikas ga al'ummar kasar.

Ya bayyana cewa, Zimbabwe za ta cimma burinta na samun bunkasuwa, duk da yakin tattalin arzikin da Burtaniya tsohuwar uwar gijiyar da ta yi mata mulkin mallaka da kawayenta suke mata.

Shugaba Mnangagwa ya kara da cewa, sama da shekaru 20 na takunkuman da kasashen yamma suka kakkabawa kasar domin ganin sun raunana tattalin arzikin Zimbabwe, da kuma tilastawa 'yan kasar tayar da kayar baya ga gwamnatin ZANU-PF mai mulki, amma har zuwa wannan lokaci, sun gaza haifar da sauye-sauyen tsarin mulki ba bisa ka’ida ba a kasar.

Ya kara da cewa, gwamnati na ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaban kasar, duk da wahalhalun da ake fuskanta a kokarin cimma wannan buri.

Don haka, ya sha alwashin cewa, gwamnatinsa za ta yi tsayin daka wajen ganin ta kare al'adun kasar. (Ibrahim Yaya)