logo

HAUSA

An sako wasu mutane biyar cikin fasinjojin jirgin kasan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Najeriya

2022-08-04 10:32:13 CMG Hausa

Rahotanni daga Najeriya na cewa, an sako mutane biyar, daga cikin mutanen da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, a wani harin da suka kaiwa wani jirgin kasa a jihar Kaduna da ke arewacin kasar, kimanin kwanaki 127 bayan faruwar lamarin.

Mutane biyar din da aka sako ranar Talata, na daga cikin fasinjojin da ba a san adadinsu ba a cikin jirgin kasan da ya taso daga Abuja a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna, da ’yan bindigar suka tare a ranar 28 ga watan Maris, a daidai lokacin da yake tunkarar babban birnin jihar ta Kaduna.

Daga cikin wadanda aka saki, akwai Farfesa Mustapha Umar Imam dake aiki a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto, da Akibu Lawal, da Abubakar Ahmed Rufa’i, da Mukthar Shu’aibu Sidi da kuma Aminu Sharif.

Kawo yanzu dai an saki mutane 37 daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.

Har yanzu akwai raguwar mutane 35, a hannun ’yan bindigar, da suka hada da tsofaffi, da mata da yara.

Shugaba Buhari dai ya bukaci jami’an tsaro, da su kara himma wajen ganin an sako su. (Ibrahim Yaya)