logo

HAUSA

Wang Yi: Batun Taiwan zai kammala ne da dinkuwar kasa

2022-08-04 14:09:43 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya ce, ayyukan tsokana da kasar Amurka ke yi, game da batun Taiwan ba bisa kuskure ba, wani shiri ne da aka tsara a tsanake, wanda kuma ya fallasa mummunar manufarta ta yaudara.

Wang Yi ya bayyana hakan ne Larabar nan, yayin da yake ganawa da firaministan kasar Cambodia Samdech Techo Hun Sen a birnin Phnom Penh na kasar.

Wang ya ce, yunkurin Amurka na dakile kasar Sin ta hanyar fakewa da batun yankin Taiwan, ba zai taba yin nasara ba, kuma ba zai canza yanayin tarihi dake tabbatar da cewa, babu makawa Taiwan zai dawo karkashin ikon kasar Sin, tare da zaburar da al'ummar Sinawa biliyan 1.4, da su hada kai, tare da gaggauta gina babbar kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani mai sigar kasar Sin. (Ibrahim)