logo

HAUSA

DRC ta yanke shawarar korar kakakin MONUSCO daga kasar

2022-08-04 13:24:59 CMG Hausa

Gwamnmatin jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC), ta bukaci mai magana da yawun tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ( MONUSCO) a kasar, Mathias Gillmann, a hukumance da ya fice daga kasarta, biyo bayan wani tashin hankali da ya barke, yayin wata zanga-zangar nuna adawa da tawagar a yankin gabashin kasar a makon jiya.

A cikin wata wasika a hukumance da ministan harkokin wajen Kongon Christophe Lutundula ya rubuta, mai dauke da kwanan watan 28 ga watan Yuli, wacce aka wallafa a safiyar ranar Laraba, hukumomin kasar sun bukaci tawagar MONUSCO, da ta yi shirye-shiryen da suka dace don  ganin Mathias Gillmann ya fice daga cikin kasar ba tare da wani bata lokaci ba, ganin yadda Gillmann ya furta wasu kalamai na rashin fahimta da ba su dace ba."

A wata hirar da aka yi da shi ranar 13 ga watan Yulin da ya gabata, a gefen taron manema labarai da MONUSCO da suka shiryawa mako-mako a Kinshasa, babban birnin kasar, Mathias Gillmann ya tabbatar da cewa, wani kaso mai yawa na albarkatun MONUSCO da sojojin Congo Kinshasa da aka tura a yakin da ake yi da 'yan tawayen M23, ya yi illa ga sauran yankunan da sauran kungiyoyin masu dauke da makamai suke gudanar da aika-aikarsu.

Kakakin gwamnatin kasar Patrick Muyaya, ya shaidawa taron manema labarai ranar Talatar da ta gabata cewa, mutane 36 ne suka mutu ciki har da dakarun MONUSCO guda uku, yayin da wasu kimanin 170 kuma suka jikkata yayin zanga-zangar. Yana mai cewa, gwamnati ta yanke shawarar sake duba yarjejeniyar janyewar tawagar ta MONUSCO, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da tawagar a yankin gabashin kasar. (Ibrahim)