logo

HAUSA

Kudin shigar kamfanonin Sin ya zarce na takwarorinsu na Amurka

2022-08-04 20:56:24 CMG Hausa

Kudin shigar kamfanonin kasar Sin dake cikin jerin manyan kamfanoni 500 na duniya, ya zarce na takwarorinsu na Amurka, karon farko a shekarar 2021.

Rahoton mujallar dake fitar da jerin manyan kamfanonin, ya ce kudin shigar kamfanonin Sin dake jerin, ya dauki kaso 31 cikin dari na jimilar kudin shigar kamfanonin 500, wanda ya zarce na Amurka da ya dauki kaso 30 cikin dari. (Fa’iza Mustapha)