logo

HAUSA

Wasu gwamnatocin kasashe da kungiyoyin duniya suna goyon bayan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya

2022-08-04 12:33:16 CMG Hausa

 

A ranar 2 ga wata ne, kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta ziyarci yankin Taiwan, duk da babbar adawar da kasar Sin ta nuna kan ziyarar. Game da wannan batu, gwamnatocin kasashe da kungiyoyin duniya sun fitar da sanarwoyi, inda suka nuna matsayinsu na goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, da nuna adawa da yadda Amurka ta keta ikon mulkin Sin da mallakar cikakkun yankunanta.

Babban sakataren MDD António Guterres ya bayyana cewa, za a tsaya tsayin daka kan kudurin kasancewar kasar Sin daya tak a duniya da aka zartar a yayin babban taron MDD, kuma wannan shi ne tushen dukkan matakan da za a dauka.

A nata bangare, ministar watsa labarai kuma kakakin gwamnatin kasar Zimbabwe Monica Mutsvangwa, ta bayyana a jiya cewar, yadda Pelosi ta ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin wani mataki ne na cin zarafi da kuma tsokana, ya kuma keta manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Haka zalika, ma’aikatar harkokin wajen kasar Eritrea ta bayar da sanarwa cewa, yadda Pelosi ta ziyarci Taiwan ta keta dokokin kasa da kasa da manufar kasar Sin daya tak a duniya. Kuma wannan wani mataki ne na rashin hankali da Amurka ta dauka a kasashen Asiya a ‘yan shekarun nan da suka gabata, wanda ya kara nuna gazawar Amurka a fannin tafiyar da manufofin duniya.

Bugu da kari, kasashen Jamhuriyar Kongo, da Sudan ta Kudu, da Sudan, Burundi, da Cuba, da Serbia, da Belarus, da Myanmar, da Thailand da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ta SCO, su ma sun nuna rashin amincewarsu da yadda Amurka ta keta ikon mulkin kasar Sin, duk da ikirarin da take yi cewa, tana mutunta manufar kasar Sin daya tak a duniya.(Kande Gao)