logo

HAUSA

Jakadan Sin da ke Jamhuriyar Nijar ya wallafa wani bayani don bayyana matsayin gwamnatin Sin kan batun Taiwan

2022-08-04 11:08:38 CMG Hausa

Jiya ne, jakadan kasar Sin da ke Jamhuriyar Nijar Jiang Feng, ya wallafa wata kasida mai taken “Tabbas kasar Sin za ta yi nasarar dunkulewar kasar waje daya” a jaridar NIGER INTER da ta LA ROUE DE L'HISTOIRE da sauran muhimman kafofin watsa labaran Nijar, inda ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin, kan ziyarar da Pelosi ta kai yankin Taiwan.

Bayanin ya nuna cewa, a kwanakin baya ne kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin, lamarin da ya aike da wata alamar kuskure ga ‘yan a-ware na Taiwan, da keta manufar kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyi guda uku da Sin da Amurka suka bayar cikin hadin gwiwa, kana ya lalata tushen dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka a siyasance, da keta ikon mallakar cikakkun yankunan kasar Sin, da kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan. Don haka kasar Sin ta nuna adawa da kakkausar murya kan wannan batu.

A cewar bayanin, tun fil azal, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. Kuma batun Taiwan, wani batu ne da ba a warware ba sakamakon yakin basasar Sin. Kasancewar babban yanki da Taiwan na kasar Sin daya ne bai taba canzawa ba kuma ba za a iya canza shi ba. Haka kuma babu wanda zai kalubalanci ka’idar kasar Sin daya tak a duniya. Amincewa da wannan manufa, ita ce tushen kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da sauran kasashe, kuma kasar Sin ba za ta taba yarda wani ya kalubalanci wannan manufa ba.

Bayanin ya kara da cewa, game da batun yankin Taiwan, ko da yaushe kasashe masu tasowa da dama ciki har da Jamhuriyar Nijar, na martaba manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma ba sa goyon bayan ‘yancin kai na Taiwan, matakin da kasar Sin ta yaba matuka.

An yi imanin cewa, sakamakon ci gaban karuwar karfin kasar Sin, da dimbin goyon bayan da take samu daga kasashe aminanta, ko shakka babu, wata rana kasar Sin za ta cimma burinta na hadewar kasar waje guda.(Kande Gao)