logo

HAUSA

Jakadan Sin a Niger ya gana da ministan harkokin wajen kasar

2022-08-03 20:27:56 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a Niger, Jiang Feng, ya gana da ministan harkokin wajen kasar, Hassoumi Massoudou, inda suka yi musayar ra’ayi game da dangantakar abota da ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Yayin ganawar, jakadan Jiang Feng ya ce a shirye Sin take ta ingiza dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.

Shi kuwa Hassoumi Massoudou, godiya ya yi wa kasar Sin game da goyon baya da taimakon da ta dade ta na bayarwa wajen inganta tattalin arzikin Niger da zaman takewa da kyautata rayuwar jama’ar kasar. (Fa’iza Mustapha)