logo

HAUSA

Shin ziyarar da Nancy Pelosi ke shirin kai wa Taiwan ba Takala ba ce?

2022-08-03 00:11:24 CMG Hausa

Ko shakka babu, burin Amurka shi ne tada hankalin duniya domin cimma wani muradi nata na kashin kai. Kuma dukkan alamu sun nuna cewa, sam ba ta kaunar zaman lafiya. A ranar Juma’ar da ta gabata, shugaban Amurka ya bayyana cewa, kasarsa na girmama manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma ba ta goyon bayan ’yancin kan yankin Taiwan. Sai dai har kullum, Amurkar kan yi amai ne ta lashe. Yayin da shugaban kasar ya bayyana haka tare da cewa hadin gwiwar Sin da kasarsa na da muhimmanci ga zaman lafiyar duniya, sai kuma aka ji shugabar majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi na shirin ziyartar yankin na Taiwan. Wannan fa na zuwa ne bayan kasar Sin ta yi gargadi da babbar murya game da hakan. Har kullum, shugaban Amurka kan furta wani abu dake karfafa gwiwar alakar kasarsa da Sin za ta kyautata domin amfanin al’ummun duniya, amma kuma, sai ’yan siyasar kasar su furta ko aiwatar da wani abu da ya sabawa hakan. Shin babu fahimta ne tsakanin shugaban kasar Amurka da sauran ’yan siyasar kasar? Ko kuma wani salo ne na makircin Amurka? Idan Amurkar ba ta sani ba, wannan yana kara zubar da kimarta ne a idon duniya. Domin a ranar Juma’a, duk da muhimman batutuwa da aka tabo, an yi tsammanin ganin kyautatuwar lamura da dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu, amma kuma batun ziyarar Nancy Pelosi, ya kawar da wannan tunani.

Duk inda Amurka ta shiga, ta tsoma baki cikin harkokinsu na gida, to ba a karewa lafiya. Ga misali nan na zahiri ana gani a kan Ukraine, lamarin da ba kasashen dake rikicin kawai ya shafa ba, har da na shiyyarsu da sauran nahiyoyi, kai da daukacin duniya.

Kasar Sin dai, ta yi gargadi game da rashin amincewarta da ziyarar ta Nancy Pelosi a yankin Taiwan. Taiwan, yanki ne mallakar kasar Sin, don hak duk wata hulda ta jakadanci ta kai tsaye da yankin, ya keta manufar Sin daya tak a duniya, da tubalin hadin gwiwar Sin da kowacce kasa, haka zalika, ya take dokokin huldar kasa da kasa. Bisa la’akari da hakan, duk wata alaka ta kai tsaye da yankin, abu daya yake nufi, wato takalar fada.

A bayyane yake cewa, burin Amurka shi ne kokarin ta da rikici a Sin, ta daidaita  al’ummar kasar sama da biliyan 1.4 dake zaune lami lafiya, da hargitsa tattalin arzikinta da tasiri da ma karfinta a duniya, sannan za ta ja gefe ta bar Taiwan, hakarta ta cimma ruwa ke nan.

A nata bangare dai kasar Sin kamar kowacce kasa mai sanin ya kamata, burinta shi ne tabbatar da dunkulewar kasar cikin lumana, sai dai kuma, hakan ba ya nufin za ta kyale ana yadda aka ga dama da yankunanta. Ta kuma nanata cewa, za ta yi dukkan mai yuwuwa, ciki har da daukar matakan soji, domin kare cikakken ’yanci da iko da yankunanta.(Fa’iza Mustapha)