logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya jinjinawa kokarin sassan kasa da kasa wajen shawo kan kalubalen tsaro

2022-08-03 11:15:14 CMG Hausa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jinjinawa sassan kasa da kasa, bisa kokarin aiwatar da matakan da suke taimakawa, wajen shawo kan kalubalen tsaro dake addabar Najeriya, da ma sauran sassan duniya daban daban.

Shugaba Buhari ya yi tsokacin ne a jiya Talata, lokacin da yake karbar takardun kama aiki na wasu sabbin jakadun kasashen waje, a fadar gwamnati dake birnin Abuja. Ya ce ana iya cimma nasarar dakile matsalolin tsaro tsakanin kasashe, idan aka yi hadin gwiwa yadda ya kamata.

Buhari ya kuma yi kira da a kara azama, wajen hada karfi da karfe domin dakile ayyukan ta’addanci, da ayyukan ‘yan fashin daji, da kuma sauran masu tada kayar baya. Ya ce kalubalen rashin tsaro a sassan duniya, da sauyin yanayi, da tasirin annobar COVID-19, sun gurgunta tattalin arzikin duniya, yayin da kasashe daban daban ke ci gaba da fadi-tashin farfadowa daga wadannan tarin matsaloli.

Ya ce "Najeriya na tare da sauran kasashe, yayin da muke ta hankoron kawar da ayyukan ‘yan fashin daji, da masu garkuwa da mutane, da tashe tashen hankula masu alaka da rikicin manoma da makiyaya, da sauran masu tada kayar baya, a daya bangaren, muna samun karin nasarori da tallafin kasashe abokan mu. Za mu ci gaba da kara azama, har sai mun shawo kan dukkanin kalubale”.  (Saminu Alhassan)