logo

HAUSA

NDLEA ta gano wasu wurare da ake sarrafa sinadarin methamphetamine a Lagos da Anambra

2022-08-03 10:59:25 CMG Hausa

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ko NDLEA Mohamed Buba Marwa, ya ce hukumar sa ta gano wasu wurare guda biyu a jihohin Lagos da Anambra, da ake amfani da su wajen sarrafa kwayar methamphetamine.

Marwa, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana jiya Talata a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, ya ce NDLEA ta yi nasarar kwace tarin sinadarai da ake amfani da su wajen hada wannan kwaya. Kaza lika an cafke mutane 3, da suka hada da mamallaka wuraren da ake gudanar da wannan mummunar sana’a su 2, da kuma wanda ke hada musu kwayar.

Ya ce jami’an hukumar sun yi nasarar cafke mutanen ne a ranar Asabar. Har ila yau, sun gano kwayoyin methamphetamine da nauyin su ya kai kilogiram 258.74, da sauran sinadarai da ake hada kwayar da su.  (Saminu Alhassan)