logo

HAUSA

Dole ne Amurka ta dauki alhakin lalata zaman lafiya a yankin zirin tekun Taiwan

2022-08-03 10:45:55 CMG Hausa

Duk da rashin amincewa da kasar Sin ta nuna da babbar murya, kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta kare aniyarta ta zuwa yankin Taiwan na kasar Sin a jiya Talata da dare, matakin da ya kasance barazanar siyasa, sakamakon yadda ta daga matsayin mu’amala a tsakanin Amurka da Taiwan, wanda kuma hakan ya sabawa manufar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwoyin hadin gwiwa guda uku a tsakanin Sin da Amurka, kuma hakan ya lalata tushen huldar Sin da Amurka, tare da lalata mulkin kan kasar Sin, da ma cikakkun yankunanta, kana mugun mataki ne wanda zai haifar da sakamako mai tsanani.

Kari kan hakan, mataki ne da ya sake shaida cewa, wasu ’yan siyasar Amurka dake goyon bayan ’yan aware na Taiwan, sana fatan lalata zaman lafiya, da kwanciyar hankali a yankin zirin tekun Taiwan, da na duniya baki daya. Sai dai tabbas, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba, don kare ikon mulkin kanta, da ma cikakkun yankunanta.

Batun Taiwan na shafar babbar moriyar kasar Sin, kuma kasancewarta ta uku a jerin manyan jami’an gwamnatin Amurka, tabbas Pelosi tana sane da hakan, amma kuma ta yi kunnen-uwar-shegu, a yunkurin cimma moriyarta ta fannin siyasa, ba tare da yin la’akarin da abin da matakin zai haifar ga huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, da tsaron shiyya, da ma Amurka ita kanta ba. Matakin da kuma ya kara fahimtar da gamayyar kasa da kasa, irin yadda mahukuntan yankin Taiwan ke dogara ga kasar Amurka wajen cika burin ballewarsu, da ma yadda ’yan siyasar Amurka ke amfani da batun Taiwan wajen dakile kasar Sin.

A wani bangaren kuma, yadda Pelosi ta kawar da kai daga bin gaskiya, ya kara tsananta yanayin da ake ciki a yankin, tare da haifar da barazana ga zaman lafiya a yankin Asiya da tekun Pasifik. Lallai kam, cin amana take yi yadda Amurka ta yi amai ta lashe, da ma nuna fuska biyu a kan batun, zai ingiza saurin dakushewarta. (Lubabatu)