logo

HAUSA

Kamata ya yi kasashen dake da tarin makaman nukiliya su fara ragewa bisa adalci in ji wani jami’in kasar Sin

2022-08-03 15:42:13 CMG Hausa

 

Jami’in hukumar dake lura da warware makaman nukiliya ta kasar Sin Fu Cong, ya ce kamata ya yi kasashen dake da tarin makaman nukiliya su wuce gaba, wajen rage makaman yaki da suke da su, a fayyace, tare da kaucewa sake kara mallakar wasu, kuma su yi hakan bisa tsarin doka.

Jami’in ya bayyana hakan ne ga mahalarta taron bita, na sassan da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya karo na 10. Yana mai cewa "Yayin da ake kwance damarar makaman nukiliya, kamata ya yi a wanzar da daidaito tsakanin kasa da kasa, da samar da tsaro mai dorewa ga kowa".  (Saminu Alhassan)