logo

HAUSA

Jami’an Namibiya: Takunkumin da kasashen yamma suka kakaba wa kasar Rasha ya kara tsananta karancin abincin Afirka

2022-08-02 15:44:26 CMG Hausa

A kwanakin nan ne, minista mai kula da aikin gona, da ban ruwa da kuma aikin gyara gonaki na kasar Namibiya Calle Schelttwein, ya nuna yayin wata hirar da ya yi da wakilin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, cewar yanzu tasirin takunkuman da kasashen yamma suka kakkaba wa kasar Rasha, sun kara tsananta rikicin abinci a Afirka, kana sun haifar da mummunan tasiri a fannonin makamashi da abinci da sana’ar raba kayayyaki da sauransu.

A kasashen Afirka, yawancin kudaden shigar da jama’a ke samu, na tafiya ne wajen sayen abinci, kuma mutane da dama ba za su iya samun isashen abinci ba sakamakon hauhawar farashin abinci. Don haka, yana fatan za a gaggauta warware rikicin Rasha da Ukraine ta hanyar diplomasiya da tattaunawa cikin lumana. (Safiyah Ma)