logo

HAUSA

Jami’an diflomasiyyar Afirka na fatan kara kulla huldar tattalin arziki da kasar Sin

2022-08-02 10:40:13 CMG Hausa

Jami'an diflomasiyya 29 daga kasashen Afirka 15 sun ziyarci yankin gwaji na shirin zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka a lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin daga ranar 27 zuwa 29 ga watan Yuli. Jami’an sun kuma bayyana imaninsu kan tattalin arzikin kasar Sin suna masu fatan kara kulla huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashensu da kasar Sin.

Duk da tasirin barkewar annobar COVID-19 da ake ta fama da ita, gami da sarkakiya da yanayin da duniya ke ciki, jami'an diflomasiyyar sun bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da juriya, kuma kasuwar kasar na cike da damammaki. Inda suka bayyana fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin aikin gona, da tattalin arziki na yanar gizo da kiwon lafiya.

A cewar jakadan Tanzaniya dake kasar Sin Mbelwa Kairuki, kasuwar kayayyaki ta kasar Sin mai yawan jama’a biliyan 1.4, tana da damammaki masu tarin yawa ga dukkan kasashen Afirka.

Alkaluman kididdigar da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar na nuna cewa, darajar ciniki tsakanin Sin da Afirka, ta kai dalar Amurka biliyan 254.3 a shekarar 2021, karuwar kashi 35.3 cikin 100 kan makamancin lokaci na shekarar 2020, inda Afirka ta fitar da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 105.9 zuwa kasar Sin, wanda ya karu da kashi 43.7 cikin dari. (Ibrahim Yaya)