logo

HAUSA

Abubakar Abdullahi Gaya: Ina kwadayin koyon yaren Sin!

2022-08-02 14:52:22 CMG Hausa

Abubakar Abdullahi Gaya, ko kuma Wang Sicong a yaren kasar Sin, wani matashi ne mai shekaru 20, wanda ke zaune a jihar Kanon tarayyar Najeriya, wanda ya karanci harshen Sinanci daga shekara ta 2015 zuwa ta 2020, a makarantar koyon yaren Sin dake garin Kwankwaso a Kano.

A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Abubakar Abdullahi Gaya, ya bayyana yadda makarantarsu take, da kalubalen da yake fuskanta, a yayin da yake kokarin koyon yaren kasar Sin.

Har wa yau, ya bayyana fahimtarsa kan wasu al’adun gargajiyar kasar Sin, da rawar da yaren Sin ke takawa a fannin sada zumunta tsakanin kasar Sin da kasashen duniya, musamman Najeriya. (Murtala Zhang)