logo

HAUSA

Shugaban Kenya Ya Yaba Da Hanyar Mota Da Kamfanin Sin Ya Shimfida

2022-08-02 15:35:21 CMG Hausa

Kwanan nan, aka fara aiki da tagwayen hanyar mota dake birnin Nairobi hedkwatar kasar Kenya a hukumance, wadda kamfanin shimfida gada da hanya na kasar Sin wato CRBC ya zuba jari, tare da gina ta. Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya halarci bikin kaddamar da hanyar, inda ya yaba da yadda hanyoyin mota da kamfanonin kasar Sin suka shimfida, wajen magance matsalar cunkuson ababan hawa a birnin na Nairobi matuka.