logo

HAUSA

Bisa aiki tukuru Sin ta samu karbuwa a kasashen Afirka

2022-08-02 21:03:57 CMG Hausa

A baya bayan nan, tawagar masana ta kasar Kenya, mai lakabin "Cibiyar raya tattalin arzikin yankin gabashin Afirka", ta fitar da rahoto, na sakamakon wani bincike game da tasirin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka.

Rahoton ya yi nuni da yadda kasashen Afirka ke jinjinawa ingancin ababen more rayuwa da Sin ke ginawa a nahiyar, da saurin aiwatar da manufofi, da kammala ayyuka a kan lokaci.

Dalilai na zahiri sun tabbatar da cewa, Sin na aiwatar da matakai masu nagarta da inganci, ta kuma samar da moriya mai yawa, da damammaki na ingiza ci gaban Afirka, matakin da ya samar mata da amincewa da yabo. (Saminu Alhassan)