logo

HAUSA

EAC ta kaddamar da tawagar sa ido kan zaben Kenya

2022-08-02 11:01:55 CMG Hausa

Jiya ne, kungiyar kasashen gabashin Afirka (EAC) ta kaddamar da tawagar sa ido kan zaben kasar Kenya da za a gudanar a ranar 9 ga watan Agusta.

Shugaban tawagar sa ido kan zaben na EAC a babban zaben Kenya na shekarar 2022, Jakaya Mrisho Kikwete, ya shaidawa manema labarai a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, tawagarsa ta kunshi mambobi 52, wadanda aka zabo daga manyan hukumomi da cibiyoyi masu zaman kansu na kasashe abokan hulda da kungiyoyin al'umma.

Ya ce, “a matsayinmu na yanki, muna da yakinin cewa, sanya ido a yankin na da matukar muhimmanci, wajen kara sahihancin zabuka, da karfafa ayyukan kungiyoyin sa ido na cikin gida, da kara karfafa gwiwar jama'a, kan daukacin tsare-tsaren zaben.

A mako mai zuwa ne, ake saran ‘yan kasar Kenya za su kada kuri’a, domin zabar sabon shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin kasar, da gwamnoni da majalisun kananan hukumomi 47 na kasar.

Za a fafata a zaben na watan Agustan da muke ciki ne, tsakanin manyan kawancen siyasa biyu wato Kenya Kwanza, karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar William Ruto, da Azimio la Umoja wanda tsohon Firaminista Raila Odinga ke jagoranta, wanda ke samun goyon bayan shugaba Uhuru Kenyatta.(Ibrahim)