Yadda mazauna unguwar Gida kamar Irin Ruman suke rayuwa
2022-08-01 20:19:47 CMG Hausa
A unguwar "Gida Kamar Irin Ruman" dake yankin masana'antu na garin Chapcha, na gundumar Gonghe ta lardin Qinghai, Pu Xinghua, 'yar kabilar Han ce, take koya wa wasu mata ‘yan asalin kabilun Tibet, Hui, Mongolian da kuma Salar fasahar zane-zane. Da zuwanmu, Pu Xinghua ta ce, "Mu ‘yan uwa ne muna son juna."
Mata daban- daban dake unguwar, suna amfani da lokacin hutun da suke da shi, don koyan fasahohin saka iri daban daban.
Gou Xiaohong, wata 'yar kabilar Tibet ta ce: "Ana sayar da kayayyakin da aka saka da hannu irin su matashin kai, zanen ado da sauransu ta kafar bidiyo da kuma a zahiri, wanda ke taimaka mana waje samun kudin shiga a kofar gida."
Unguwar masana’antu tana da gidaje 1,416 da mutane 4,268 daga kabilu daban-daban da suka hada da Han, Tibet, Hui, Mongolian, Salar, Man, da Miao da dai sauransu, ana iya cewa, unguwa ce mai kabilu daban-daban.
Ma Jinshan, 'yar asalin kabilar Hui mai shekaru 70, ta zo zauren hidimar al'umma don ba da rahoton matsalolin da ake fuskanta a gidanta ga ma'aikatan, ta ce, "Ɗana kurma ne kuma ba shi da tsayayyen aiki, ko za ku taimaka wajen magance wannan matsalar?"
Rencuoji, ‘yar kabilar Mongolian, ita ce ma’aikaciyar sashen jin kai na unguwar “Gidan Irin Ruman”, ta rubuta abubuwan da Ma Jinsha ta fada, kuma ta gaya mata cewa, za ta gabatar da matsalolin ga babbar ma’aikata, do haka sai ta jira kira. Ma Jinshan tana rike da hannun Rencuoji cikin farin ciki, ta ce, “Na gode sosai yarinya! Gaskiya kuna kula da mu sosai, kuna da kirki.”
Jing Zhuo, darektar kwamitin unguwannin jama’a na unguwar masana'antun, ta bayyana cewa, saboda unguwar Xigoutai ta tsuffa sosai, don haka jama'a su kan gamu da "bacin rai" kamar fasa bututun ruwa da kuma toshe magudanan ruwa, wani lokaci kuma, za a iya samun ‘yan rikici tsakanin makwabta. Yang Xinglin, dan Tibet da ya yi ritaya daga aiki, ya kasance "mai shiga tsakani na sa kai tsakanin al'umma", kullum yana magance kananan rikice-rikicen dake faruwa a tsakanin ‘yan kabilu daban daban. Yang Xinglin ya ce, "Yanzu an samu raguwar rikice-rikice, kuma mazauna wurin sun fahimci juna kuma suna da tawali'u, kana kowa ya fahimci cewa, 'idan an yi hakuri da juna, to za a samu sakamako mai kyau'."
Tawagar raye-raye ta "Gidan Irin Ruman" tana yin atisayen raye-rayen kabilar Tibet a unguwar Chengxi da ke garin Chapcha a gundumar Gonghe. Shugaban kungiyar raye-rayen, Kuan Taiji ta gabatar da cewa, kungiyar raye-rayen ta kunshi mutane daga kabilun Han da Tibet da Hui da sauran kabilu, mafi tsufa a cikinsu shi ne mai shekaru 47 da haihuwa, yayin da mafi karanci shekaru, shi ne mai shekaru 24. Ta kara da cewa, "Muna gudanar da wasannin al'adu a ranar sabuwar shekara, bikin bazara da sauran bukukuwa. Raye-rayen na kabilar Tibet, da na Mongoliya da kuma raye-rayen irin na Yangko, shirye-shirye ne da muka tsara."
Baya ga haka kuma, a lokacin bikin bazara, bikin sabuwar shekara bisa kalandar Tibet, da kuma sallar idi da sauran bukukuwan gargajiya, su kan shirya al'ummomin kowane kabilun da ke cikin unguwar, don su fafata da juna, a fannoni wasannin al'adu, gasar ilimi da sauran ayyuka, hakan yana karfafa yin cudanya da mu'amala tsakanin kabilu daban daban, da karfafa fahimtar ra’ayin raya al'ummar kasar Sin cikin hadin kai.
Ga iyalai masu fama da wahalhalu irin su gidaje masu fama da talauci, gidajen da iyaye suke aiki a waje, da kuma iyalai dake uwa daya a yankin, unguwar “Gidan Irin Ruman” ta bude wani ajin kula da yara a lokacin hutu, inda yara daga kabilu daban daban za su rika shakatawa tare a cikin unguwar.
Limaocuo, 'yar Tibet mai shekaru 11 da haihuwa, a halin yanzu tana karatu a makarantar firamare dake gundumar Gonghe. Gani cewa, mahaifinta ba ya tare da ita, kuma mahaifiyarta tana aiki a cikin gundumar, don haka, ajin kula da yara ya zama "gida" a gare ta a lokacin hutu. A nan ta koyi rawa, fasahar rera waka, zane-zane, kwallon kwando, tsalle-tsalle, da sauransu tare da sauran yara.
Li Na, malamar ajin kula da yara, ta ce a lokacin da Limaocuo ta fara zuwa ajinsu, ba ta son yin magana, amma tare da tallafin malamai da dalibai, yanzu ta canja.
A unguwar “Gidan Irin Ruman”, duk wanda ke cikin matsala, za a yi kokari don a taimake su. Ma Jinwen mai shekaru 86 dan kabilar Hui da ke zama shi kadai, an kwantar da shi a asibiti saboda rashin lafiya. Da samu wannan labarin, mazauna da ma’aikatan unguwar sun kai masa abinci bisa ga al’adar kabilarsa bi da bi. Bayan an sallame shi daga asibiti, sai aka kai shi a cibiyar kulawa ta rana, ba tare da bata lokaci ba ma’aikatan unguwar suka kai masa kudin tallafi na kusan yuan dubu daya. Tsoho Ma Jinwen ya yi godiya sosai ga ma’aikatan unguwar, a cewarsa, sun fi kusanci da danginsa.
Ju Mo, mai shekaru 72 a duniya ya ce, yana da babban iyali, shi ‘dan kabilar Salar ne, matarsa kuma ‘yar kabilar Hui ce, surukarsa ‘yar kabilar Han ce. A duk lokacin bikin bazara, sabuwar Shekarar Tibet, da sallar idi, dukkan iyalin suna murnar bikin tare. A ganinsa, "Iyalin suna zama tare, suna ci tare, suna kuma son juna, suna rungumar juna kamar irin rumman."