logo

HAUSA

Wakiliyar MDD a Libya mai barin gado ta damu da yadda ake siyasantar da kamfanin mai na kasar

2022-08-01 09:43:32 CMG Hausa

 

Mai ba da shawara ta musamman ga babban sakataren MDD a Libya dake shirin barin gado, Stephanie Williams ta bayyana damuwarta game da yunkurin da ake yi na siyasantar da hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasar (NOC).

A yayin jawabinta na karshe, Uawargida Williams ta yi na’am da kokarin da kasar ta yi, na ganin an dawo da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, bayan shafe fiye da shekaru goma ana fama da rikici, amma ta lura cewa, ya kamata hukumomin kasar su sami ’yancin kai.

Ta ce, ta yarda da cire dage shingen hana fitar da man fetur din da aka sanyawa kasar, amma ta damu da kokarin da wasu ke yi na neman siyasantar da kamfanin mai na kasar (NOC).

A baya-bayan nan ne kamfanin ya sanar da sake bude rijiyoyin man kasar da tasoshin ruwa, bayan shafe kusan watanni 3 da masu zanga-zangar suka rufe. Hakan ya haifar da karuwar yawan man da ake hakowa.

A tsakiyar watan Afrilu, masu zanga-zangar cikin gida, suka rufe rijiyoyin mai da tasoshin ruwa da dama a Libya, inda suka bukaci firayim minista Abdul-Hamed Dbeibah ya mika mulki ga gwamnatin da majalisar dokokin kasar ta nada a watan Maris. (Ibrahim)