logo

HAUSA

Kasashen Afirka ba su iya samun isassun alluran rigakafin cutar kyandar biri da suke bukata ba

2022-08-01 11:23:32 CMG Hausa

 

Jami’an kiwon lafiyar jama’a na gargadin cewa, yunkurin da kasashe masu sukuni ke yi na sayen allurar rigakafin cutar kyandar biri masu tarin yawa, da kuma yadda suka ki raba alluran rigakafin cutar da kasashen Afirka, na iya barin miliyoyin mutane ba tare da kariya daga cutar dake da hatsari da kuma hadarin ci gaba da yaduwar kwayar cutar a cikin mutane.

Masu sukar wannan lamirin suna fargabar sake maimaita matsalar rashin adalci da aka gani, yayin barkewar cutar COVID-19.

Dr. Boghuma Kabisen Titanji, mataimakiyar farfesa a fannin likitanci a jami'ar Emory na ganin cewa, an riga an maimaita irin kurakuran da muka gani yayin bullar COVID-19. Tana mai cewa, yayin da kasashe masu arziki suka yi odar miliyoyin alluran rigakafi, don dakile cutar a kan iyakokinsu, a gyefe guda kuma, babu kasar da ta sanar da shirin raba alluran tare da kasashen Afirka, inda nau'in cutar kyandar biri ke yaduwa fiye da kasashen yamma.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) tana bullo da tsarin raba alluran rigakafin ga kasashen da abin ya shafa, amma kuma bayanan da ta fitar game da yadda za ta yi aiki kalilan ne. Bugu da kari, babu wani tabbaci daga hukumar, game da ba da fifiko ga kasashe matalauta a Afirka. Tana mai cewa, kawai za a ba da alluran rigakafin cutar ne bisa la'akari da bukatu na annoba.

Ya zuwa yanzu dai, an samu rahoton bullar cutar kyandar biri sama da 22,000 a kasashe kusan 80 tun daga watan Mayu, inda ake zargin mutane kusan 75 ne suka mutu a Afirka, galibi a kasashen Najeriya da Kongo. (Ibrahim)