logo

HAUSA

Guterres ya nuna fushi kan lamarin kisa da ya faru a Congo Kinshasa

2022-08-01 14:56:02 CMG Hausa

A jiya ne, babban sakataren na MDD Antonio Guterres ya sanar ta hannun kakakinsa, inda ya nuna fushi matuka kan yadda jami’an wanzar da zaman lafiya na MDD suka yi harbi a kan yankin iyakar Congo (Kinshasa) da Uganda, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane biyu, tare da jakkata wasu. Mummunan lamarin da aka ce ya fusata shi, inda ya kira da a hukunta wadanda ke da hannu a cikn lamarin.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Guterres ya yi maraba da matakin da wakilinsa a Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo ya dauka, na tsare jami'an tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (MONUSCO) wadanda ake zargi da hannu a lamarin tare da gudanar da bincike nan take.

Wata sanarwar da gwamnatin Kongo Kinshasa ta fitar a jiya na cewa, da safiyar ran 31 ga watan Yuli ne wasu dakarun MONUSCO suka bude wuta a Kasindi dake kan iyakar lardin Arewacin Kivu na Kongo Kinshasa da Uganda, saboda an hana su tsallaka iyaka. Lamarin ya haddasa kisan mutane 2 tare da jikkata wasu 15.

Gwamnatin Kongo Kinshasa da tawagar MONUSCO sun kaddamar da wani bincike tare domin binciko dalilin da ya haddasa lamarin, sannan za a yanke hukunci mai tsanani kan wadanda ke da hannu cikin lamarin. (Safiyah Ma)