logo

HAUSA

Shugaban Zambia ya ziyarci rumfar Sin a taron baje kolin harkokin noma da kasuwanci na kasarsa karo na 94

2022-08-01 20:25:56 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema, ya halarci taron baje kolin harkokin noma da kasuwanci na kasar sa karo na 94, inda ya ziyarci rumfar kasar Sin, irinta ta farko da Sin din ta kafa a baje kolin.

Taken baje kolin na bana shi ne "Fasaha ke ingiza kirkire kirkire-Fasaha ke sauya kasuwanci".

A bana baje kolin na Zambia, ya samu tarin kamfanonin Sin mahalarta, cikin kamfanoni kusan 110, wadanda suka shafi sassa daban daban, kamar fannin shuka tsirrai, da sarrafa na’urorin aikin gona, da na sarrafa albarkatun noma. (Saminu Alhassan)