logo

HAUSA

Shugaban Kenya Ya Yaba Da Hanyar Mota Da Kamfanin Sin Ya Shimfida

2022-08-01 11:21:25 CMG Hausa

Jiya ne, aka fara aiki da tagwayen hanyar mota dake birnin Nairobi hedkwatar kasar Kenya a hukumance, wadda kamfanin shimfida gada da hanya na kasar Sin wato CRBC ya zuba jari, tare da gina ta.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya halarci bikin kaddamar da hanyar, inda ya yaba da yadda hanyoyin mota da kamfanonin kasar Sin suka shimfida, wajen magance matsalar cunkuson ababan hawa a birnin na Nairobi matuka.

A cikin jawabin nasa, Kenyatta ya ce, tagwayen hanyoyin na Nairobi da kuma sabuwar hanyar mota da ta kewaye gabashin Nairobi da aka kammala ginawa a ranar 31 ga watan Yuli, za su daidaita matsalar cunkuson motoci a birnin Nairobi matuka. Kafin fara aiki da tagwayen hanyoyin, sai an shafe kalla sa’o’i 3 a mota a wasu sassan birnin, amma yanzu mintuna 15 zuwa 24 ne kawai.

Shugaban ya kara da cewa, tun bayan gwada fara aiki da hanyar motar daga ranar 14 ga watan Mayu, hanyar ta taka rawa sosai, ta kuma taimakawa Nairobi shiga zamanin rage lokacin zirga-zirga, da kara yin mu’amala tsakanin mutane, da rage cunkuson motoci da inganta ayyuka. Haka kuma ta samar da muhallin kasuwanci mai kyau, lamarin da zai kara samar wa Kenya damammaki a fannonin yawon shakatawa, da shirya tarurruka da sha’anin otel-otel.

James Macharia, ministan zirga-zirga da ababen more rayuwar jama’ar Kenya ya bayyana yayin bikin cewa, tagwayen hanyar mota dake Nairobi tana daya daga cikin ababen more rayuwar jama’a mafi inganci a Afirka, kana kuma abin misali ne a fannin hadin gwiwa a tsakanin gwamnatin Kenya da kamfanoni masu zaman kansu. (Tasallah Yuan)