logo

HAUSA

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta MDD ta ayyana Kenya a matsayin kasa ta biyu mafi tsaro a filayen jiragen sama

2022-07-31 16:32:09 CMG Hausa

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta duniya ta MDD (ICAO), ta sanya Kenya a mataki na biyu a nahiyar Afrika, a matsayin wadda tafi tabbatar da tsaro a filayen jiragen samanta.

Cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Asabar a Nairobi, hukumar kula da jiragen sama ta kasar Kenya, ta ce kasar ta kai wannan mataki mafi koli na tabbatar da tsaro a fannin harkokin sufurin sama a yankin gabashin Afrika ne, biyo bayan wani bincike da hukuamr ICAO ta MDD mai mambobi 93 ta aiwatar a watan mayu.

Hukumar ICAO ta ba Kenya maki na kaso 91.7, wanda ya karu kan kaso 88 da ta kasance a shekarar 2015, saboda aiwatar da wasu muhimman tsarukan sufurin jiragen sama. Wannan maki shi ne mafi yawa da aka taba samu a yankin gabashi da tsakiyar Afrika, haka kuma, ya sanya Kenyar a mataki na biyu bayan kasar Afrika ta kudu dake mataki na farko. 

Hukumar ICAO ta yi rangadi ne a manyan filayen jiragen sama biyu na kasar da suka hada da filin jiragen sama na kasa da kasa na Jomo Kenyatta dake Nairobi da takwaransa na Moi dake Mombasa.

Manufar binciken tsaron ita ce, tabbatar da tsaron fasinjoji da ma’aikatan cikin jirgi da na filin jiragen da sauran al’umma a filayen. (Fa’iza Mustapha)