logo

HAUSA

Kenya ta gargadi shafin Facebook game da kalaman kiyayya

2022-07-31 16:30:45 CMG Hausa

Majalisar hadin kan kasa ta Kenya, ta gargadi shafin sada zumunta na Facebook game da kalaman kiyayya, tana mai bukatarsa da ya rika daukar mataki kan kalaman kiyayya cikin kwanaki 7.

A cewar majalisar, kasar za ta dakatar da shafin daga aiki a kasar, idan ya gaza daukar mataki.

Hukumomi a kasar kenya sun gano cewa, Facebook ya gaza yin nazarin da ya kamata, inda yake kyale tallace-tallacen kiyayya cikin harshen Swahili da Ingilishi.

Har ila yau, majalisar ta ce, Facebook din, ya keta dokokin kasar, kuma ya bari ana amfani da shi wajen yayata kalaman kiyayya da haddasa fitina da bayanan karya da na bogi. (Fa’iza Msutapha)