logo

HAUSA

​An Kaddamar Da Tagwayen Hanyar Da Kasar Sin Ta Gina A Kudu Maso Yammacin Kamaru

2022-07-30 15:30:13 CMG Hausa

Jiya ne, aka kaddamar da wata babbar hanyar mota da kasar Sin ta gina a kudu maso yammacin Kamaru.

Da yake jawabi a yayin bikin kaddamar da aikin, ministan ayyukan jama'a na kasar Kamaru, Emmanuel Nganou Djoumessi ya bayyana cewa, bude hanyar ya kawo karshen kammala matakin farko na babbar hanyar Kribi zuwa Lolabe.

Yana mai cewa, babbar hanyar za ta saukaka zirga-zirgar ababen hawa da ta mutane daga kowane sashe na kasar zuwa tashar ruwan Kribi mai zurfi.

A nasa jawabin ministan kudi na kasar Louis Paul Motaze, ya bayyana cewa, hanyar wadda kamfanin aikin injiniya na kasar Sin mai suna China Harbour Engineering Company (CHEC) ya gina, ta samo asali ne daga hadin gwiwar kut da kut da ke tsakanin kasashen Sin da Kamaru.

Mataimakin babban manajan kamfanin CHEC reshen yankin Afirka ta Tsakiya Zhang Wenfeng,ya bayyana cewa, babban layin da ke kan hanyar Kribi zuwa Lolabe, yana da tsawon kilomita 38.5, kana yana da hanyoyi guda shida, inda aka kebe biyu da ke tsakiya don amfani a nan gaba.

Zhang ya kara da cewa, fara aiki da babbar hanyar, zai inganta yanayin kasuwanci a kasar Kamaru, da kara samar da ayyukan yi, da hanyar tattalin arziki mai haske a fadin kasar.(Ibrahim)