logo

HAUSA

Shin Wane Ne Ya Danawa Kasashen Afrika “Tarkon Bashi”?

2022-07-29 17:01:53 CMG Hausa

Jaridar The Guardian ta Birtaniya, ya fitar da wani rahoto a baya-bayan nan, da ya yi kira ga cibiyoyin bayar da bashi na yammacin duniya, su saukaka tsarin biyan basussukan da suke bin kasashe masu karancin kudin shiga, musamman kasashen Afrika.

Wannan rahoton na zuwa ne bayan cibiyar Debt Justice ta Birtaniyar, mai bibiyar yadda ake bayar da bashi tsakanin kasashen duniya, ta bankado wasu alkaluma dake nuna cewa, basussukan da cibiyoyin kudi na yammacin duniya ke bin kasashen Afrika, ya rubanya wanda kasar Sin ke binsu har sau 3, haka kuma kudin ruwansu ya ninka na Sin sau biyu.

Tambayar a nan ita ce, shin wane ne ya danawa kasashen Afrika Tarkon Bashi?

Batun “Tarkon Bashi” wani abu ne da kasashen yamma suka kirkiro, bisa zargi mara tushe da suke wa kasar Sin da kakabawa kasashen Afrika bashi fiye da kima. Sai dai, sun tsallake tarin basussuka da kudin ruwa da cibiyoyin kudi na kasashensu suka laftawa kasashen na Afrika.

Karya fure take ba ta ’ya’ya. Yanzu ga gaskiya ta fito, amma kasashen masu neman haifar da kiyayya tsakanin Sin da aminanta na Afrika, kawai saboda kishin karbuwar da ta samu, sun yi gum.

Duk wanda ya je kasashen na Afrika, zai ga yadda kasar Sin ta taimaka wajen gaggauta samar da kayayyaki na ci gaban da kyautatuwar rayuwa, daga kayayyakin more rayuwa, zuwa zuba jari da samar da aikin yi da tallafin karatu da na lafiya da bunkasa cinikayya da kafa kamfanoni, har ma da dakarun wanzar da zaman lafiya da sauransu. Hakika in ma bashi ne, an gani a aikace, domin duk wani katafaren aikin ci gaba a kasashen, za a ga cewa mafiya yawansu, Sin ce ta aiwatar. Duk da dimbin bashi da kasashen yamma suke bin kasashen, ba a ga wani abun a zo a gani da suka tabuka ba.  

Bayan barkewar annobar COVID-19, kasar Sin ta amsa kiran kungiyar G20 na saukaka lokacin biyan bashi ga kasashe masu karancin kudin shiga, inda kawo yanzu ta sassauta biyan sama da dala biliyan 1.3, wanda ya dauki kaso 30 na jimilar shirin. Wannan ya sa kasar Sin ta zama kan gaba wajen aiwatar da shirin. A don haka ne ma, cibiyar Debt Justice ta yi kira ga kasashen yamma su tilastawa cibiyoyinsu na kudi aiwatar da shirin kamar dai yadda Sin ta yi.

Ina laifin mai taimakawa da kasancewa da kai a kowanne yanayi? Kasar Sin ta kasance mai amsa kiran kasashen Afrika a ko da yaushe, mai nuna kulawa a gare su, mai kare muradunsu a dandalin kasa da kasa, mai kai musu dauki cikin gaggawa, haka kuma mai jansu a jiki da yayata gogewarta gare su. Wadannan kadan ne daga cikin dalilan da ya sa kasashen ke kara aminta da ita. Kamar yadda shugaban Nijeriya ya taba furtawa da aka masa tambaya game da bashin kasar Sin, kofarsa a bude take ga duk wanda ke son taimakawa kasarsa, kuma kasar Sin ta kasancewa mai taimaka mata cikin sauki ba tare da sharadi ko katsalandan ba. Kuma shakka babu, irin hakan ne ke kasancewa a wajen dukkan kasashen nahiyar.  (Fa’iza Mustapha)