logo

HAUSA

Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram 20 a arewa maso gabashin Najeriya

2022-07-29 11:08:35 CMG Hausa

A kalla mayakan kungiyar Boko Haram 20 ne sojojin Najeriya suka hallaka cikin makwanni 2 da suka gabata, yayin da sojojin kasar suka kaddamar da matakan yaki da ’yan ta’adda a yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin rundunar sojojin Najeriya Bernard Onyeuko, ya shaidawa manema labarai hakan a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Yana mai cewa, yayin samamen, wasu mayakan kungiyar da iyalansu kimanin su 2,016 sun mika wuya ga sojoji a sassa daban daban na yankin.

Jami’in ya kara da cewa, daga farkon shekarar bana zuwa yanzu, mayakan kungiyar Boko Haram, da na ISWAP, da iyalansu 55,000 ne suka mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya.

Bugu da kari, Onyeuko ya ce cikin wadanda suka samu ’yanci bayan samamen sojojin, akwai mata da yara da dama, ciki har da ’yan matan sakandaren Chibok biyu da aka sace tun a ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014, an kuma kubutar da su ne a garin Aulari dake arewacin jihar Borno dake shiyyar. (Saminu Alhassan)