logo

HAUSA

An yi kira ga cibiyoyin bayar da bashi na kasashen yamma su saukaka basussukan dake durkusar da kasashen Afrika

2022-07-29 11:24:31 CMG Hausa

Wani rahoton jaridar The Guardian ta Birtaniya, ya ce kamata ya yi cibiyoyin bayar da bashi na yammacin duniya, su saukaka tsarin biyan basussukan da suke bin kasashe masu karancin kudin shiga, domin fitar da su daga matsalar bashi.

A cewar cibiyar Debt Justice mai bibiyar harkokin basussuka, bankuna da masu kula da kadarori da masu cinikin man fetur na kasashen yamma, na bin gwamnatocin Afrika basussukan da yawansu suka zarce wanda kasar Sin ke binsu. Tana mai cewa, an yi kuskuren dorawa kasar Sin laifin gazawa wajen kyautata tsarin bayar da bashi, maimakon kasashen yamma.

Rahotanni sun ruwaito Tim Jones, shugaban cibiyar Debt Justice na cewa, shugabannin kasashen yamma, na dora laifin yawan bashin da ake bin kasashen Afrika kan kasar Sin, amma hakan, yunkuri ne na karkatar da hankali daga kansu. Ya ce gaskiyar batu shi ne, bankunansu da masu kula da kadarori da ma masu cinikin man fetur, su ne ke da alhaki, amma kungiyar G7, ta yi biris da batun.

Ya kara da cewa, gwamnatocin kasashen yamma sun kasa tabuka komai kan kamfanonin dake kasashensu, ba kamar Sin ba, sun gaza saukaka tsarin biyan bashin a lokacin annobar COVID-19, yana mai bukatar Amurka da Birtaniya, su samar da dokar da za ta tilasta cibiyoyin bayar da rance masu zaman kansu, su shiga cikin shirin saukaka lokacin biyan bashin. (Fa’iza Mustapha)