logo

HAUSA

Mugun matakin Amurka a tekun kudancin kasar Sin ba zai yi nasara ba

2022-07-29 15:48:13 CMG Hausa

Nan da kusan wata guda, kasar Amurka ta aiwatar da mataki a tekun kudancin kasar Sin, na aika jiragen ruwan yaki zuwa kofar yankin kasar Sin don ta da hankali. A waje guda kuma, ta yi wa kasar Sin batanci, wanda ya sa ta daukar matakin kariya na halal ala tilas, ta mayar da kasar a matsayin “mai zafin kai”.

A matsayinta na wata kasa dake nesa da shiyyar, Amurka ta nuna karfinta a kan tekun kudancin kasar karkashin tutar "’yancin zirga-zirga" na tsawon shekaru da dama, wanda shi ne babban dalilin da ya sa ake son inganta aikin soja a tekun kudancin kasar Sin.

A bayyane take, Amurka ta yi matukar keta hurumin kasar Sin da tsaronta, kuma ta yi mummunar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, amma ta sanya hular “mai zafin kai” da ta dinka saboda kanta a kan kasar Sin, wadda ke kiyaye mulkin kai da tsaron kasa, da nufin dora laifi kan Sin, da tsokanar dangantaka tsakanin Sin da makwabtanta wadanda dukkansu suke bakin tekun kudancin Sin, ta yadda za a tayar da rikici a yankin.

Shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 20 da rattaba hannu kan sanarwar matakan bangarori daban daban da suka shafi tekun kudancin kasar Sin. A cikin shekarun 20 da suka gabata, dukkan bangarorin sun bi sanarwar a tsanake, tare da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, tare da kiyaye 'yanci da tsaron zirga-zirga a yankin. Yanzu, kasashen yankin sun kware da himma, da jagorancinsu, wajen magance faruwar hadaruka a yankin tekun kudancin kasar Sin. Duk yadda Amurka ta yi taguwar ruwa a yankin, za ta zama kamar guguwar ruwa da ke tahowa, kuma ba za ta cimma nasara ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)