logo

HAUSA

Antonio Guterres ya nada Abdou Abarry a matsayin wakilin sa a janhuriyar Afirka ta tsakiya

2022-07-29 15:53:49 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya sanar da nadin Abdou Abarry daga janhuriyar Nijar, a matsayin wakilin sa, kuma shugaban ofishin shiyya na MDD a janhuriyar Afirka ta tsakiya ko UNOCA a takaice. Abarry ya maye gurbin Francois Lounceny Fall daga kasar Guinea.

Cikin sanarwar da ya gabatarwa manema labarai game da sabon nadin, Mr. Guterres ya godewa Fall bisa jajircewarsa, da aiki tukuru, a tsawon wa’adin jagorancin UNOCA na shekaru biyar da rabi.

Kafin nadin na sa, Mr. Abarry shi ne wakilin dindindin na janhuriyar Nijar a ofishin MDD dake birnin New York. Ya kuma taba rike mukamin wakilin musamman na shugaban kungiyar tarayyar Afirka AU, kuma babban jami’in ofishin wakilci na AU a janhuriyar dimokaradiyyar Congo. (Saminu Alhassan)